Yadda wani makaho kuma kurma yake sana'ar fawa a garin jos


Wani bawan Allah mai suna Muhammadu zubairu dattijo ne da yake da shekaru a duniya wanda yake sana’ar fawa duk da lalurar da Allah ya dora mashi bai zama rago ko dan maula ba, yana fita kasuwa domin nemarwa kansa halal dinsa.


Wannan bayan Allah da gidan jaridar Rfihausa nayi fira da shi lalura biyu ne da shi inda gashi makaho baya gani gashi kurma domin kura Wata ‘yarsa ce ke jiyar da shi maganar mutane.


Malam Muhammadu zubair makaho mai sana’ar fawa a zantawarsa da dan jarida yana mai cewa


Wannan lallurar ya same ni akan aiki nane , a can baya lafiya lau nake gani daga bayane abun ya same ni da kwanta ko na kama wayo,nayi kokarin nemo magani Allah bai bani Sa’a ba, domin nayi yawo daga karshe ba barwa Allah komai.”

Tayaya kake wannan sana’a bayan alhali yanzu baka gani?

” Yanzu haka hankuri da idon dai nazo nayi sana’a  na nemi abinda zanci”

Kuma lallurar bata hanaka sana’ar ba?

“Eh haka dai nake ta hakuri ina sana’ar duk da bana gani, idan  na samu ya warka  na kama gani kuma shikenan.

Yanzu kamar wane irin taimako kake bukata?


Eh to taimako da nake so daga gurin Allah suna da yawa , tunda ina da yara da suke makaranta , ina zaune a gidan haya, ina neman inda zan biya kudin gidan haya da kuma na chi da iyalina.

Wane irin taimakon gaggawa kake so a yi maka ?

Taimakon gaggawa duk a wurin Allah ne , ya kawomin wanda zan samu kudin da zanje na samu maganin idon sai in tafi, domin  abun na Allah sai ayi dace, idan kuma na samu gidan da zan zauna duk Allah ne mai bayarwa.


Post a Comment

Previous Post Next Post