Wani matashi wanda a baya ya dade yana bayyana soyayyarsa ga jarumar Kannywood, Maryam Yahaya ya bayyana yadda wata mata ta yi amfani da soyayyarsa ga jarumar don cimma manufarta.
Shafin TikTiko wani suna El- shanawa masoyin Maryam Yahaya ya wallafa bidiyonsa inda yake cewa:
“Wani babban masoyin Jaruma Maryam Yahaya mai suna El-Shanawa dan Jihar Jigawa, ya fada cikin halin ha’ula’i sanadiyyar soyayyar da yake wa Maryam Yahaya.
Amma ku saurari bidiyon kuji daga bakinsa, don batun ba zai fadu ba. Ance waka a bakin mai ita ta fi dadi.”
Kamar yadda ya bayyana a wani bidiyo, cike da alhini yace matar ya nuna masa cewa za ta hada shi da jarumar wanda hakan yasa ya shirya ya nufi garin Kano.
Ya bayyana yadda ta zo da mota ya dauke shi inda ta rufe shi a gida har yayi kwana uku zuwa hudu duk tana ce masa Maryam din tana wasu ayyuka.
Daga bisani ta bayyana masa cewa zata hada shi da Maryam amma ta waya don jarumar tana wasu ayyuka ne ashe duk ba gaskiya bane.
Ya ci gaba da shaida cewa, ya shiga yanayin da bai taba shiga ba rayuwarsa kuma yana fatan Ubangiji ya gafarta masa tunda ba da son ransa hakan ya auku ba.