AMARACI KENAN....
Amarachi Ma'aikaciya ce a Banki, tana bangaren marketing, shekarunta 32
Kafin ta kashe kanta, ta rubuta wannan wasika, tana mai nuna yanke tsammani game da rayuwar duniya
A cewarta rayuwar tayi tsanani a Nigeria, ba zata iya jurewa ba, don haka ta zabi barin duniyar, tana mai bawa iyayenta hakurin rasa ta
Ta shiga Bandaki a Bankin da take aiki, sai ta sha guba, aka zo aka tarar da gawarta a Bandakin, a halin yanzu 'yan sanda suna kokarin tabbatar da rubutun hannunta don gano ko ita ta rubuta
Matsalar shine Amaraci bata san abinda zata je ta tarar ba, na tabbata da sai ta zabi kuncin rayuwar duniya akan na lahira
Shiyasa Sheikh Aminu Daurawa yace mutum ba addini dabba yake komawa, fahimtar addini da mu'amalartan Qur'ani shine maganin kowani irin damuwa da kunci
Allah Ya tsare mana imanin mu