Hukumar tace finafinai da dab'i ta jihar Kano karkashin jagorancin Abba El Mustapha ta kai sumamen kama masu siyar da maganin gargajiya


Hukumar tace finafinai da dab'i ta jihar Kano karkashin jagorancin Abba El Mustapha ta kai sumamen kama masu siyar da maganin gargajiya wadanda ake zarginsu da furta kalaman da basu dace ba.

Sumamen ya gudana ne cikin wasu kasuwannin cikin gari dana kauye da suka hada da Kasuwar Garin Gabasawa, Gezawa, Larabar Mata , Kasuwar Sabon Gari da kuma Kasuwar Ƙofar Wambai. 

Yayiin wannan sumamen jami'an hukumar sun samu nasarar kama kimanin mutane goma sha biyu tare da kuma kayan da suke amfani dasu wajen tallan.

Shugaban hukumar Abba El mustapha ya bayyana cewa, idan har masu gudanar da wannan kasuwanci na siyar da magungunan basu daina amfani da kalaman da basu dace ba, to tabbas hukumar ba zata daga kafa ba.

A nasu bangaren wadanda ake zargi da siyar da wadancan magungunan, sun karbi laifinsu tare da kuma neman afuwa ga hukumar.

Rahoto: Abdulmubdiu Ado Abubakar

Post a Comment

Previous Post Next Post