Duka dai jam'iyyun APC da NNPP suna tsaka mai wuya a jihar Kano


Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP ne ya ɗaukaka zuwa kotun koli, kan hukuncin kotun daukaka kara da ya ce ɗan takarar jam'iyyar APC Nasiru Yusuf Gawuna ne ya yi nasara.

Magoyan bayan jam'iyyun, suna ci gaba da addu'o'i da saukar Alƙur'ani a mazaɓu da ƙananan hukumomi.

Dakta Faruk Kuwa, shugaban hukumar NADA wanda dan jam'iyyar NNPP ne ya ce suna da kwarin guiwar wannan karon alkalan za su yi adalci sabanin abun da suke zargin an musu a baya.


Muna kyautata zaton cewa alkalai a wannan kotun koli za su yi adalci su tabbatar wa al'ummar Kano abun da suka zaba, dama nan ne cibiyar dimukradiyya, jama'a sun fito sun zabi gwamna Abba Kabir kuma Allah ya ba shi nasara, don haka muna fatan za a tabbatar wa jama'a abun da suka zaba'' in ji shi.

Alhaji Ibrahim Zakari Sarina, shine sakataren jam'iyyar APC a jihar Kano, kuma ya bayyana cewa a nasu bangaren suma suna nasu addu'o'in.

''Mun yi addu'a, mun je kotu, kuma Allah isashshe ne, kuma ita ma kotu ba za ta tsallake hujjuji da dalilan da muka gabatar ba, don haka muna kyautata zaton nasara na tare da su'' a cewarsa.


A ranar 17 ga watan Nuwamba ne kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja babban birnin ƙasar ta kori ƙarar da gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya shigar a gabanta, yana ƙalubanlantar hukuncin da kotun ƙararrakin zaɓe ta yanke.

Kotun ƙararrakin zaɓen ta ce Nasiru Yusuf Gawuna na APC ne ya lashe zaɓen gwamnan da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris, ba Abba Kabir usuf na NNPP ba.

Sai dai gwamna Abba Kabir da jam'iyyarsa ta NNPP sun garzaya kotun koli domin ƙalubalantar hukuncin.

Ba wai al'ummar jihar Kano ne kadai suka zuba ido suna jiran ganin yadda wannan hukunci zai kasance ba, harma da na sassan kasar baki daya, kasancewar kallon da mutane da dama ke yi wa Kano a matsayin cibiyar siyasar arewacin Najeriya.

Dukkan bangarorin NNPP da APC dai sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar amincewa da duk hukuncin da kotun kolin za ta yanke domin tabbatuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar ta Kano.

Post a Comment

Previous Post Next Post