Hukumar Hajji ta jihar Zamfara ta fara mayarwa maniyyata 504 kudadensu naira miliyan 747.

Hukumar Hajji ta jihar Zamfara ta fara mayarwa maniyyata 504 kudadensu naira miliyan 747.

Maniyattan sun biya kudaden ne ga hukumar tsakanin shekarar 2019 zuwa 2023.

Musa Mallaha, shugaban hukumar ya ce Gwamna Dauda ya bada umurnin a fara biyan kudin daga Disamba zuwa Fabrairun 2024.

Malam Mallaha ya ce hukumar za ta sa naira miliyan 92 kari kan kudin da gwamnan ya amince a mayar. "Gwamna ya amince da mayar da naira miliyan 747 ga wanda abin ya shafa cikin biya uku tsakanin Disambar 2023 zuwa Fabrairun 2024 
Zancen da na ke yanzu, gwamna ya biya naira miliyan 218 na watan Disamba don biyan kaso na farko. "Tuni an tura kudin zuwa asusun hukumar Hajji", in ji shi Ya ce kudin zai zama kari kan naira miliyan 92 da ke asusun hukumar kafin fara rabawa wanda za su ci gajiyar. "Za mu fi mayar da hankali ga wanda su ka nuna sha'awar zuwa hajjin 2024, musamman wanda suka ajiye wani kudi a hukumar", in ji Malam Mallaha. Shugaban hukumar ya yi alkawarin yin aiki da gaskiya ya yi gudanar da aikin, ya kuma yaba wa gwamnan bisa yadda ya bai wa hukumar kula.

Post a Comment

Previous Post Next Post