A gaskiya Na Yi Murna Da Tinubu Ya Ƙara Farashin Man Fetur – shugaba Buhari



Tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ya yi murna matuƙa da shugaban ƙasar na yanzu, Bola Ahmed Tinubu ya ƙara farashin man fetur a ƙasar.

Buhari ya faɗi haka ne a yayin wani taro da ƙungiyar tuntuɓa ta jihar Katsina ta shirya da manufar ƙaddamar da yaƙi da tu’ammali da miyagun ƙwayoyi a tsakanin ƴan jihar.


Jaridar Jakadiya na ruwaito,a yayin taron wanda ya gudana a ranar Lahadin nan a fadar gidan gwamamtin jihar ta Katsina, cikin raha da barkwanci tsohon shugaban ya ce,…



Na san wahalar Najeriya da daɗinta na sani, Alhamdulillahi, na dawo gida na zauna mutane na ta zuwa suna gaida ni a kullum.”

“Da Tinubu ya ƙara kuɗin mai ina murana saboda baƙi zasu ragu, amma sai suka shirya sai su tara kuɗin man sai su faɗo ma ni.” Inji shi ya faɗa a cikin raha.

Daga ƙarshe kuma tsohon shugaban ya yi kira ga masu riƙe da madafun iko a dukkan matakai da su kasance masu riƙon amana.


Post a Comment

Previous Post Next Post