Wannan labarin marar daɗi ne ga duk wani mai imani da kishin keta hakkin bil’adama inda ake lalata mata wanda babu gaira ba dalili.
Wani matashin mai amfani da shafin sada zumunta mai suna Isma’il Ibrahim El-kanawy ya wallafa wannan rubutu mai matukar tada hankalin al’umma irin yadda ake kashe mutane arewa da kuma yi musu abin bakin ciki da takaici ga abinda ya wallafa a shafinsa.
Ana ta debe yaran mu mata ana lalata musu rayuwa, amma shugabannin mu babu abinda ya dame su balle su nuna damuwar su, amma wani katon arnen mawaki ya mutu a Lagos sun mike a majalisa saboda girmama mutuwarsa…
Allah ya isan mu wallahi, Allah Ka saka mana”
Hausaloaded ta tattaro martanin Mutane da sukayi tsokaci akan wannan rubutun.
@murjanatu Ibrahim marafa cewa take :
Amin Yah Rabbi.
Ai saboda ba yan yaran su bane, ko MATAN su.
Addu’a itace kawai magani,
Last week ɗan uwa na, ya fito hannun su, amma wlhy ya Koma kamar mahaukaci saboda bakar azabar da ya sha, da kuma ganin yanda suke walakanta Mata
.yah Rabbi ya kawo mana agaji, ya saka mana ga duk wani azzalumi. AMIN.
@bello king khan cewa yake :
musanman shuwagabanni mu ma arewa. Babu abinda ya damesu. In kaga sundamu şuna magana toh abinda zai taba kujerar su ce.
@zaharaddeen Muhammad cewa yake:
Ai idan kana neman mutanen da ba su san ciwon kan su ba ,toh idan ka samu ‘Yan Arewa ka gama,komai na mu babu hadin kai a ciki
Allah ta’ala ya kawo mana agajin sa.
@Abubakar bashir cewa yake:
Ai idan kana neman tumaki kasami shuwagabannin arewa magana ta kare… Sai dai Allah yasaka mana.
@Armiya’u yusuf goronyo cewa yake:
Ameen Ya mujibudda’awat.kuma muna addu’a Allah Ya jarabce su da irin wannan musibar.